Khuraira Musa’s biography, net worth, fact, career, awards and life story

Is Artist 
Businessperson 
From Nigeria 
Type Arts 
Business 
Gender female
Birth Lere, Nigeria

Khuraira Musa yar’Najeriya ce, mazauniyar Amurka, ta kasance shahararriyar kuma kwararriyar mai-kwalliya ce, shafe-shafe da kuma taimakon alumma, itace wacce ta samar kuma shugaba ce ta kamfanin Khuraira Cosmetics. Khuraira ta shahara a fagen kwalliya da shafe-shafe na duniya, wanda ta kasance tana gudanar da ajujuwan koyarwa ga mutane daga duniya baki daya. A rayuwar ta tayi kwalliya ga shahararrun mutane kamar su, Brandy, Mandy Moore, Paula Abdul, Kirstie Alley, Natalie Cole, Cher, Suzanne Douglas, Trista Rehn da kuma Dr. Suzanne Rice.

Farkon rayuwa da aiki

Khuraira Musa an haife ta a Ƙaramar hukumar Lere Jihar Kaduna, Najeriya. Ta rasa mahaifiyar ta a lokacin haihuwar ta, wanda hakan ne yasa ta rayu a gidan rainon marayu dake yankin Rukuba/Bassa a Jihar Plateau, amma bayan nan ta koma jihar Kaduna har sai da ta kammala makarantar sakandare. A 1992 taje kwaleji a Tarayyar Amurka wanda anan ne ta fara aiki a shaguna.

Aikin agaji

Khuraira Musa ta kafa gidauniyar da ake kira da suna Arewa Development Support Initiative (ADSI) hukuma wacce bata gwamnati ba, da niyyar taimakawa cigaban matasa da mata a yankin Arewacin Najeriya. Gidauniyar na tallafawa da samun karatu ga mata, sana’o’in hannu da dabarun kasuwanci. Khuraira itace ta samar da makarantar Zainab Memorial saboda karantar da marasa karfi musamman marayu waɗanda ke a Bassa/Rukuba a Jihar Plateau.

Manazarta

Wannan ƙasida guntu ne: yana buƙatar a inganta shi, kuna iya gyarashi.

Hanyoyi na waje

  • “Official website Khuraira Cosmetics”
You May Also Like